Yadda tauraruwar Naziru Laja ke ci gaba da haskawa a Enugu Rangers

Rahotanni sun bayyana tauraruwar tsohon dan wasan Rivers United Naziru Auwal Laja, na ci gaba da haskawa a kungiyar da ya koma ta Enugu Rangers.

Independent Mirror ta rawaito Naziru Laja a sabuwar kakar wasanni ta bana ya buga karawa biyu da Rangers tayi a gasar NPFL.

Dan wasan da a baya ya bugawa Rivers United, wadda ta lashe gasar Firimiya a kakar 2021 tare da Nasiru Laja din.

Laja a wasan farko da kungiyarsa ta Enugu Rangers tayi da Remo Stars sunyi rashin nasara da ci 2-1.

Sai dai a mako na biyu da suka kece raini a karshen mako da Doma United Rangers din ta yi nasara da ci 2-1 a wasan na gasar Firimiya ta kasa NPFL ta kakar 2023/2024.

A gefe guda matashin Dan wasan, na daya daga wadanda suke wakiltar Najeriya, a matakin Yan kasa da shekara U23 a tawaga ta kasa.

Domin kuwa ya buga wasan share fagen da tawagar Najeriya Yan kasa da shekara U23 tayi da kasar Tanzania.

Haka zalika ma ana kallon Dan wasan nada damar ci gaba da samun nuna kansa musamman damar shiga tawagar Super Eagle ta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *