AS Garde Nationale ta kammala daukar dan wasan Barau Football Academy Nana Abraham

Kungiyar kwallon kafa ta AS Garde Nationale da ke Niamey, a jamhuriyar Niger, ta gabatar da tsohon dan wasan Katsina United Nana Razak Abraham a matsayin aro na shekara daya data dauka.

Independent Mirror ta rawaito cewa Nana Razak Abraham, tuni ya isa Niamey daga kungiyar Barau Football Academy da ke nan jihar Kano.

Kungiyar ta Barau Football Academy nada cikin kungiyoyi a nan Kano, da suke fafata wasa a gurabe da dama domin samun damar zakulo matasan yan wasa masu hazaka.

Shugaban kungiyar ta Barau Football Academy, Ibrahim Shitu Chanji ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya aikowa Independent Mirror mai kwanan watan 09 ga Oktoban 2023.

Nana Abraham, Mai shekara 20 tuni ya kasance da yan wasan kungiyar ta AS Garde Nationale domin fara daukar horo a birnin Niamey.

Nana Abraham
Nana Abraham

Dan wasan tsakiya Nana Abraham ana saran zai Rika daukar kudi Dubu 450 000 duk wata, kuma jumullar kudin da kungiyoyin suka amince da juna na shekara kan Nana ya kai sama da Miliyan Biyu da Rabi.

Nana Razak a baya ya bugawa kungiyar Katsina United da ke nan Najeriya, kafin daga bisani ya je kasar Iran domin bugawa wata kungiya.

AS Garde Nationale na daga cikin kungiyoyin da suke buga wasa a babbar gasar Tamaula a Niamey, Niger.

Haka zalika kungiyar dai an kafa ta ne a shekarar 1974, kuma a kaka biyu da suka gabata AS Garde Nationale ce ta lashe gasar Niger Premier League da kuma Niger Cup.

AC na buga wasa a filin Stade Général Seyni Kountché, mai cin Yan kallo kusan 35,000.

Kungiyar kuma na buga manyan gasar nahiyar Africa da suka hada da gasar CAF Champions League da CAF Confederation Cup.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *