Akwai son rai da son zuciya a hukuncin kotun kararrakin zaben Gwamnan Kano-NYPG

Kungiyar ci gaban Matasan Arewacin kasar nan ta Northern Youth Patriotic Group, ta ce akwai son rai da son zuciya a hukuncin kotun sauraren karrakin zaben gwamnan Gwamnan Kano da akayi a ranar Laraba.

Independent Mirror ta rawaito cewa shugaban kungiyar Injiniya Aminu Adam Takai ne ya bayyana hakan, a taron manema labarai da ya gudana a nan Kano a ranar Asabar.

Aminu Adam Takai ya ce akwai bukatar ayi duba na tsanaki kan yadda hukuncin ya gudana, domin akwai rashin adalci a cikinsa matuka.

”Abun da akai na soke kuri’u kimanin 165, 663 na kuri’un gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP tsantsar rashin adalci ne bisa maganata ta agskiya”

”Idan kuwa har za’a soke wadannan kuri’u to kamata ya yi a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, bisa cewa kuri’un da aka soke sun fi tazarar abin da aka ce an ci zaben da su ”.

Yace bai kamata wasu cikin al’umma su yi murnar wannan nasara ba , saboda hakan ya nuna cewa basu san yadda dokar zabe take ba, kuma hakan ya nuna sun nuna goyon bayan rashin adalci ne.

Injiniya Aminu Adam Takai ya kuma bukaci banagaren shari’a a kasar nan, da ya dauki matakin da ya dace domin bai wa mai gaskiya abarsa.

A makon da muke shirin bankwana da shi ne dai, kotun sauraren kararrkin zaben gwamnan Kano ta ayyana Nasir Gawuna a matsayin halastaccen gwamna a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *