Ganduje ya yi ta’aziyyar rasuwar Daraktan Kannywood Aminu S. Bono

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar daraktan fina-finan Hausa Aminu Surajo Bono.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawuna, Edwin Olofu ya fitar a ranar Talata Ganduje ya ce ya kaɗu matuka da samu labarin rasuwar wannan shararran darakta.

Ganduje ya ce rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono ba ƙaramin rashi ba ne ga masana’antar Kannywood, kuma ta bar babban gibi a masana’antar.

Kuma tuni akayi janaizar Marigayi Aminu S Bono a birnin Kano a ranar Talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *