Yanzu haka Kotun sauraren kararrakin zaben Gwamnan Kano Kano ta ayyana ranar Laraba 20 ga Satumbar 2023 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan korafi game da zaben gwamnan jihar.
Independent Mirror Hausa ta ruwaito cewa matakin na zuwa ne bayan karar da jam’iyyar APC reshen Kano ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Kano da aka zaba a ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Sai dai ana kallon Shari’ar na cikin manyan kararrakin zaben gwamna da ke daukar hankali a Najeriya.
Da fari APC dai ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaben gwamnan Kano da halastattun ƙuri’u ba.
APCn ta kuma ce akwai kuri’un da aka soke, wadanda yawansu ya zarce ratar da ke tsakanin kuri’un da Abba Kabir Yusuf ya samu da mai biye masa wato Nasiru Yusuf Gawuna Dan takarar gwamann APC.
Haka zalika wani karin korafi da APC ta yi shi ne wanda aka ayyana cewa Abba Kabiru Yusuf ya ci zaben, Kuma babu sunansa a cikin rijistar jam’iyyar NNPP.
Bugu da kari APCn ta Kuma yi korafin cewa Jam’iyyar NNPP ba ta gudanar da zaben fitar da gwani ga masu neman takara kafin zaben gwamnan Kano ba.
Independent Mirror Hausa ta bibiyi yadda bangarorin APC da NNPP ke rubutun na has ashen yiwur samun nasara a shari’ar zaben na Gwamnan Kano.
Inda matashi Ayman Ado wanda ke biyayya ga tsagin Malam Shekarau, amma an hango yadda yake adawa da tsarin Kwankwasiyya tare da nuna goyan bayan bangaren APC.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook Ayman ya wallafa wani sako kamar haka.
Hasashe Na :
Kashi na daya (i)
“Kotun tribunal dake jihar kano, ta sanya gobe laraba, 20th september domin yin hukunci akan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun akan zaben gwamna da aka gabatar a wannan shekarar ta 2023.
Jam’iyyar APC ta gabatar da koke guda uku, zamu fara da guda daya.
Jam’iyyar APC tayi zargin an shigar da wasu kuri’u na bogi ma’ana marasa stampi ko sa hannu ko serial numba kuma babu kwanan wata ajikinsu, a zaben gwamna da ya gabata.
Bisa wannan dalili ne lauyoyin APC suka bukaci kotu ta umarci hukumar zabe akan ta bada dama abi diddigin kuri’un nan da aka lissafa.
Kotu ta amsa wannan bukatar, inda da lauyoyin jam’iyyar APC da na NNPP da kuma wakilan hukumar zabe sukayi aikin zagaya wasu kananan hukumomi tare da chaje kuriun dake ajiye.
A iya zagayen da aka gabatar an samu kuri’u guda 165,616 (votes) wadanda suka shiga cikin wancan lissafin, kuma an gabatarwa da kotun Tribunal wadannan kuri’u a matsayin hujja.
Wadannan kuri’u gabadayansu dan takarar NNPP aka zaba dasu, To idan har lauyoyin APC suka iya gamsar da mai shari’a cewa wadannan kuri’u na bogi ne.
Domin kuwa har ta kai ga matakin soke su a cikin lissafi , to dan takarar APC zai samu nasara da kuria dubu dari takwas da chasa’in da yan kai (890,000+).
Dan takarar NNPP zai sakko zuwa mataki na biyu da kuri’a dubu dari takwas da hamsin da yan kai (850,000+) kamar yadda lissafin Dr.Harbau ya nuna.
A wannan zaben da aka gabatar na 2023, A jihar Benue akan kujerar dan majalisar dattijai mai wakiltar arewa maso gabashin jihar Benue, Dan takarar PDP Gabriel Suswan ya garzaya gaban tribunal akan zargin an shigar da kuriun bogi a akwatunan zabe guda 474 a kananan hukumomi guda biyar.
Dan takarar PDP ya gabatarwa da Tribunal hujjoji guda 1181, tare da shaida guda 19, Ita kuma APC ta gabatar da hujjoji guda 3 tare da shaida guda 1 , ita kuma hukumar zabe ba ta gabatar da shaida ko guda daya ba.
A karshe Alkali ya yarda cewa kuri’un nan na bogi ne, a nan take kotu tace a zaftare wadannan kuri’un na bogi daga cikin lissafi.
An kwashe kuri’u 51,892 daga cikin kuria 135,573 na dan takarar APC. Haka itama PDP aka kwashe kuri’a 21,229 daga cikin kuri’u 112,231 da take dasu.
A karshe PDP ta zama ta daya da kuri’a 90,590 , ita kuma APC ta sakko zuwa mataki na biyu da kuri’a 82,590.
Idan misalin haka ta faru a Kano, to ka da kowa yayi mamaki. Haka idan hakan bata faru ba to lauyoyin APC ne suka kasa gamsar da kotu cewa wadannan kuri’un na bogi ne.
Ni nawa kawai bincike da hasashe ne. Tabbatarwa kuma aikin Allah ne.
Ya kamata kowa ya san wannan!
Sai mun hadu a kashi na biyu, inda zanyi bayani akan wani koken.
Ni ne naku Ayman Ado.
A daya bangaren kuwa matashi Abubakar Lecture daga bangaren NNPP Kwankwasiyya ya wallafa nasa has ashen kamar haka.
Dalilan da zasu sanya kotun zaɓe tayi fatali da ƙarar APC a jihar Kano.
Bayan kammala babban zaɓen shekarar 2023, jam’iyyar APC a jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamna, tana kalubalantar nasarar da Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu, a zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris 2023.
Suna kafa hujja da cewar wai babu sunan Abba a rijistar jam’iyyar NNPP da aka turawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, sannan kuma sun ce wai adadin ƙuri’un da aka soke ya kamata a bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba (Inconclusive), wanda zamu iya cewa kwata-kwata basu fahimci sabuwar dokar INEC ta 2022 ba.
A cikin shekarar nan, jam’iyyar APM ta shigar da jam’iyyar LP da Peter Obi ƙara a gaban kotu, kan cewar Peter Obi ya fita daga PDP a ƙasa da kwanaki 30 ya shiga LP ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa.
Saboda suna so kotu ta soke takararsa, wanda kotu tayi watsi da ƙarar harma ta ci su tarar N400,000, suka daukaka ƙara, anan ma kotu tace dole sai dan jam’iyya ne yake da hurumi akan wannan, dan jam’iyyar ma ba kowa ba, sai wanda ya shiga zaɓen fidda gwani (primary election), idan anyi masa rashin adalci sai ya garzaya kotu.
Bari na koma batun soke ƙuri’u, a ranar zaɓe mambobin jam’iyyar APC sun dinga tayar da tazoma a rumfunan zaɓe don kada zaɓe ya gudana lafiya, domin suna so ƙuri’un kada su kai adadin da za’a iya bayyana wanda yayi nasara.
Wanda zaisa dole a tafi inkwankwulusib, ashe basu fahimci cewa sabuwar dokar tayi gyara akan haka ba, an kama tsohon MD na water board, tsohon MD na Kano line, da wani shima tsohon Kansila a Getso dake Gwarzo.
Wato dai suna so su aikata abinda Nasiru Yusuf Gawuna, Murtala Sule Garo da Lamin Sani Kawaji suka aikata a 2019, a mazabar Gama dake ƙaramar hukumar Nasarawa, wanda ya janyo Inkwankwulusib, saboda sashi na 26 na dokokin INEC.
A dokar zaɓe da aka yiwa gyara a 2022, komai yawan ƙuri’un da aka soke sakamakon rikici, to babu jam’iyyar da zata amfana dasu, kowa zai samu ZERO, kuma ba za’a maimaita zaɓe a wuraren da rikicin ya faru ba.
Wanda kuma duk ƙuri’un da aka soke a Kano, mafi yawa saboda rikici ne, wanda mambobin APC suka haddasa, lamarin da mu muna Allah wadai, domin banda haka da sai takarar da Abba ya bawa Gawuna ta wuce wadda aka samu, saboda haka a doka, APC suna wahalar da Shari’a ne, kuma ina da yaƙinin kotu ba zata barsu haka ba tare da anci tarar su ba.
INEC bata da hurumi akan wanda jam’iyya zata kawo a matsayin dan takara, haka ya faru a shekarar 2021 a jihar Kogi, lokacin da INEC ta ƙi karɓar sunan Natasha ta jam’iyyar SDP a matsayin yar takarar gwamna, kotu tace INEC bata hurumi.
Saboda sashi na 31 (2) (3) yace duk dan takarar da jam’iyya ta kaiwa INEC dole a karɓa, kuma Natasha tayi takara, sannan mu kalli batun tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan da Bashir Machina, wanda ba sai mun ja zancen ba, kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmad Lawan.
Dukda cewa shi a farko takarar shugaban ƙasa ya nema a zaɓen fidda gwani na APC ba Sanata, sannan mu kalli case din A.A Zaura da Sanata Rufa’i Hanga akan kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, Zaura yana ganin Malam Ibrahim Shekarau ne sunansa ya fito a matsayin dan takara a NNPP ba Hanga.
Amma kotu ta tabbatar da Hanga, saboda sabuwar dokar INEC da aka yiwa gyara a 2022, saboda Shekarau ya fita daga jam’iyya ne, sai jam’iyya ta maye gurbinsa da Hanga, wannan yana ƙara nuna muku hurumin jam’iyya a irin wadannan cases din.
A kundin tsarin mulkin Nigeria, sashe na 179 karamin sashi na 2 ya bayyana cewa, kafin INEC ta bayyana dan takarar da yayi nasara, dole sai ya samu nasara a kaso biyu cikin uku na ƙananan hukumomin jihar.
Ko Jihohi idan shugaban ƙasa ne, ko Sanata, ko ma Kansila ne) to ya ilahi ta ina Gawuna zai samu nasara a kotu, INEC fa ba makakku bane, jam’iyyar NNPP ta samu sama da kaso biyu cikin uku, saboda haka babu wani sashi ko wata doka da NNPP ta karya akan dan takarar gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir (gwamna a halin yanzu).
Ba zamu hana magoya bayan APC bawa kansu false hope ba, amma dai indai bisa dokokin INEC da kundin tsarin mulkin Nigeria za ayi hukuncin shari’ar zaɓen gwamnan Kano, to tabbas za’a kori ƙarar, kuma watakila sai an ci tarar su saboda ɓatawa kotu lokaci.
Domin mu a wajenmu babu bukatar ma NNPP ta gabatar da shaida, saboda dokokin INEC da kuma constitution, shi kansa dan takarar tasu, Nasiru Yusuf Gawuna, shaida ne a wajenmu, domin ya taya Abba murnar samun nasara, ya kuma alamta karɓi ƙaddararsa ta faduwa.
A karshe, ni ba masanin harkokin Shari’a bane, amma ko a karatu nayi kwasa-kwasai masu alaƙa da Shari’a, dokoki, mulki da kuma Demokradiyya, sannan kuma ni mai bincike ne kuma mai nazari ne akan al’amuran yau da kullu.
kuma hujjojin na da kawo duk tabbatattu ne babu wanda aka kirkira, amma idan mutum bai yarda ba, zai iya zuwa yayi bincike, kawai sai dai mu jira ranar yanke hukunci, domin ni wannan shi ne karo na farko da nayi magana akan wannan Shari’a, kuma ina fatan ya zama na karshe zuwa yanke hukunci a kotun sauraron ƙarar zaɓe (Tribunal).