Sanata Barau ya shigo Kano in da ya fara da ziyarar Gaisuwar mutuwa

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin Maliya CON ya ziyarci mahaifarsa Kano domin gudanar da wasu ayyuka.

Independent Mirror ta rawaito Barau Jibrin, jim kadan bayan saukarsa Kano bai wuce ko ina ba sai zuwa ta’aziyyar rasuwar kanwar mahaifiyar Dan’uwansa Baba Umaru Matawalle a unguwar Hausawa dake birnin Kano.

Sanata Barau wanda ke ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban Al’umma, ko a makwan da muke ciki ya bayar da tallafin Takin noma ga jama’ar Kano.

Barau a yayin ziyarar rasuwar kanwar mahaifiyar Dan’uwansa Baba Umaru Matawalle ya yi addu’ar samun Rahama gareta da ma dukanin al’ummar Musulmi.

Mataimakin shugaban majalisar Dattawan Sanata Barau I Jibrin Maliya CON ya samu rakiyar Mai magana da yawunsa Hon Shittu Madaki Kunchi.

Sanata Barau Jibrin da Hon Shitu Madaki
 Sanata Barau Jibrin da Hon Shitu Madaki

Haka zalika cikin yan rakiyar Sanatan akwai shugaban ma’aikatansa Prof Muhammad Ibn Abdullah da mai bashi shawara kan harkokin tsare-tsare Prof Bashir Muhammad Fagge da sauran magoya bayansa.

Sanata Barau Jibrin da Prof. Muhammad Ibn Abdallah
Sanata Barau Jibrin da Prof. Muhammad Ibn Abdallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *