Sabon mai dakkowa Gwamna Abba Kabiru Yusuf rahotannin abin da ke faruwa a ma’aikatar Ayyukan na Musamman Muhd Wasilu Kawo, ya ce zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon Amana.
Independent Mirror ta rawaito cewa Muhd Wasilu Kawo wanda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya nada Mai dakko masa rahotan abin da ke faruwa a ma’aikatar Ayyuka, ya ce zai yi duk abin da ya kamata domin ciyar da Kano gaba.
Wasilu Kawo wanda l ke gabatar da Shirin “Taskar Wasanni” a Nasara Radio 98.5 ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen Kai wa Gwamana Abba Gida-Gida rahotan duk abin da ke faruwa, domin sanar da shi ko dai ci gaba ko akasin haka da ke gudana a ma’aikatar.
“Burina shi ne na taimakawa Gwamnati da Gwamna wajen nunawa jama’a irin aikin alkairin da ake gudanarwa”
“Haka zalika idan naga anayin wani abu ba daidai ba, zanyi Kokarin sanarwa da gwamnati domin a gyara” a cewar Wasilu Kawo a zantawarsa da Independent Mirror.
Har wa yau Muhd Wasilu Kawo ya ce zai jajirce domin taimakon na kasa, Musamman fadakar dasu dukkan wasu tsare-tsare da gwamnati ta fito dashi domin taimakon al’umma
Baya ga tallata dukkan wasu ayyukan da gwamnatin ta su tayi Musamman a bangarori da dama na Kano.
A Yanzu haka ma dai Muhd Wasilu Kawo, Mamba ne a kwamitin ya da labarai na Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars mai taken sai Masu Gida.